Posts

MATSAYIN SALLAR TA HAJJUDI DA AKE A GOMAN KARSHE A WATAN RAMADAN

 BIDI'AH NE JAM'IN SALLAR TARAWIHI (ASHAM) DA TAHAJJUD - INJI KHALIFA UMAR IBN KHATTAB; KAMAR YANDA BUKHARI, MALIK... SU KA RIWAITO. YIN SALLAR NAFILA [ASHAM (TARAWIHI), TAHAJJUD...] A GIDA YA FI LADA; FIYE DA YIN TA A MASALLACI - INJI ANNABI MUHAMMAD(SAW); KAMAR YANDA BUKHARI, MUSLIM... SU KA RIWAITO. SALLAR MACE A DAKIN MIJINTA YA FI LADA AKAN SALLARTA A MASALLACI - INJI ANNABI(SAW); KAMAR YANDA AHMAD IBN HAMBAL, ABU DAWUD... SU KA RIWAITO. Khalifa Umar Ibn Khattab ya tabbatar da Jam'in Tarawihi da Tahajjud bidi'a ne. Bukhari, Malik... sun riwaito Abdulrahman Ibn Abdulqari (Sahabi kuma ministan kudin gwamnatin Umar), ya na cewa; "Wata Rana; a Ramadan, da Dare, ni da Umar Ibn Khattab mun je Masallaci, mutane su na ta sallar (Tarawihi) a Masallaci; ba'a Jam'i ba, sai Umar ya ce; bari in hadasu a bayan limami daya, sai ya hadasu Jam'i a bayan Ubayyu Ibn Ka'ab. Kashe gari (Umar) ya zo (Masallacin) ya tarar da ana Jam'in (Tarawihi), sai ya ce; yauw...