MATSAYIN SALLAR TA HAJJUDI DA AKE A GOMAN KARSHE A WATAN RAMADAN
BIDI'AH NE JAM'IN SALLAR TARAWIHI (ASHAM) DA TAHAJJUD - INJI KHALIFA UMAR IBN KHATTAB; KAMAR YANDA BUKHARI, MALIK... SU KA RIWAITO.
YIN SALLAR NAFILA [ASHAM (TARAWIHI), TAHAJJUD...] A GIDA YA FI LADA; FIYE DA YIN TA A MASALLACI - INJI ANNABI MUHAMMAD(SAW); KAMAR YANDA BUKHARI, MUSLIM... SU KA RIWAITO.
SALLAR MACE A DAKIN MIJINTA YA FI LADA AKAN SALLARTA A MASALLACI - INJI ANNABI(SAW); KAMAR YANDA AHMAD IBN HAMBAL, ABU DAWUD... SU KA RIWAITO.
Khalifa Umar Ibn Khattab ya tabbatar da Jam'in Tarawihi da Tahajjud bidi'a ne.
Bukhari, Malik... sun riwaito Abdulrahman Ibn Abdulqari (Sahabi kuma ministan kudin gwamnatin Umar), ya na cewa;
"Wata Rana; a Ramadan, da Dare, ni da Umar Ibn Khattab mun je Masallaci, mutane su na ta sallar (Tarawihi) a Masallaci; ba'a Jam'i ba, sai Umar ya ce; bari in hadasu a bayan limami daya, sai ya hadasu Jam'i a bayan Ubayyu Ibn Ka'ab. Kashe gari (Umar) ya zo (Masallacin) ya tarar da ana Jam'in (Tarawihi), sai ya ce; yauwa (madalla) da wannan bidi'ar, (sai Umar ya kara da cewa); mutum ya yi sallar (Tarawihi, Tahajjud... shi kadai) a karshen Dare ya fi (Lada) akan ya yi (jam'inta) a farkon Dare (bayan sallar Isha'i)":
2010 حَدَّثَنَا عَبْدُ اللَّهِ بْنُ يُوسُفَ، أَخْبَرَنَا مَالِكٌ وَعَنِ ابْنِ شِهَابٍ، عَنْ عُرْوَةَ بْنِ الزُّبَيْرِ، عَنْ عَبْدِ الرَّحْمَنِ بْنِ عَبْدٍ الْقَارِيِّ، أَنَّهُ قَالَ: خَرَجْتُ مَعَ عُمَرَ بْنِ الْخَطَّابِ(رَ) لَيْلَةً فِي رَمَضَانَ إِلَى الْمَسْجِدِ، فَإِذَا النَّاسُ أَوْزَاعٌ مُتَفَرِّقُونَ، يُصَلِّي الرَّجُلُ لِنَفْسِهِ، وَيُصَلِّي الرَّجُلُ فَيُصَلِّي بِصَلَاتِهِ الرَّهْطُ، فَقَالَ عُمَرُ: إِنِّي أَرَى لَوْ جَمَعْتُ هَؤُلَاءِ عَلَى قَارِئٍ وَاحِدٍ لَكَانَ أَمْثَلَ. ثُمَّ عَزَمَ فَجَمَعَهُمْ عَلَى أُبَيِّ بْنِ كَعْبٍ، ثُمَّ خَرَجْتُ مَعَهُ لَيْلَةً أُخْرَى وَالنَّاسُ يُصَلُّونَ بِصَلَاةِ قَارِئِهِمْ، قَالَ عُمَرُ: نِعْمَ الْبِدْعَةُ هَذِهِ، وَالَّتِي يَنَامُونَ عَنْهَا أَفْضَلُ مِنَ الَّتِي يَقُومُونَ. يُرِيدُ آخِرَ اللَّيْلِ، وَكَانَ النَّاسُ يَقُومُونَ أَوَّلَهُ.
- صحيح البخاري : كتاب : صلاة التراويح. | باب فضل من قام رمضان : (2010).
- موطأ مالك (301).
Idan jam'i sallar tarawihi Sunnah ne; me ya sa Khalifa Umar ya kira shi bidi'ah?
Ko Khalifa Umar Jahili ne; bai san Jam'in Sunnah ba ne, don haka ya kira shi bidi'ah? Kenan Umar ya jahilci kasancewar jam'in Sunnah; don haka ya kira shi bidi'a?
Ko masu cewa Jam'in Tarawihi Sunnah ne; sun fi Umar sannin Sunnah?
Lokacin da Umar ya kira jam'in tarawihi bidi'ah; akwai SAHABBAI da yawa a gurin, idan har shi Umar ya jahilci kasancewar jam'in Sunnah ne; me ya sa SAHABBAN da ke gurin ba su gyara masa ba; su ce ai Sunnah ne jam'in? Ko dai su ma Sahabban jahilai ne? Kenan kun fi Sahabbai sanin Sunnah?
Idan kun ce Umar ya na nufin jam'in sallar mtarawihi da tahajjud bidi'ah ne a lugga ba'a isdilahi ba, kenan bidi'ah kala biyu (2) ce; akwai ta lugga da isdilahi?
Daman akwai wata ka'ida ta banbance bidi'ah a lugga da istilahi?
To menene makomar hadisin كل بدعة ضلالة (Kowacce bidi'ah bata ce)?
Kenan ba ko wace bidi'ah ce bata ba?
Shin shi Umar ne da kansa ya ce a lugga ya ke nufi ba a isdilahi ba? Ko a hadisin ne aka nuna hakan? Kenan tawili ku ke yiwa hadisin? Dama kun yarda da tawili?
Tunda Umar ya tabbatar da jam'in tarawihi bidi'ah ne, kuma kun ce dukkan bidi'a bata ce, kuma dan bidi'ah dan wuta ne, kenan duk mai yin sallar tarawihi a jam'i dan Bidi'ah ne kuma dan wuta ne?
Idan Jam'in Tarawihi da Tahajjud Sunnah ne, me ya sa aka daina yin jam'in a lokacin Khalifa Abubakar?
Kenan Abubakar ya hana Sunnar Annabi(saw)?
Me ya sa Sahabbai a lokacin Abubakar ba sa yin Jam'in tarawihi? Kennan dai su ma sun jahilci kasancewar sa Sunnah?
Ko sun watsar da Sunnah?
Me ya sa duk malaman Tarihi, Hadisi... su ka ce Umar ne ya kirkiri jam'in tarawihi?
Bukhari, Muslim, Malik... sun riwaito Ibn Shihab ya na cewa;
"Har Annabi(saw) ya yi wafati ba'a Jam'in Sallar Tarawihi, sannan ba'a Jam'in Sallar Tarawihi a lokacin Khalifa Abubakar da farkon khalifanci Umar:
2009 ...قَالَ ابْنُ شِهَابٍ: فَتُوُفِّيَ رَسُولُ اللَّهِ(صَ) وَالْأَمْرُ عَلَى ذَلِكَ، ثُمَّ كَانَ الْأَمْرُ عَلَى ذَلِكَ فِي خِلَافَةِ أَبِي بَكْرٍ وَصَدْرًا مِنْ خِلَافَةِ عُمَرَ(ر). - صحيح البخاري : كتاب : صلاة التراويح. | باب فضل من قام رمضان. (37, 2008). موطأ مالك : كتاب : الصلاة | الترغيب في الصلاة في رمضان : 300. صحيح مسلم : كتاب : المساجد ومواضع الصلاة | باب : الترغيب في قيام رمضان وهو التراويح : 759 ( 174 ) ( 759 ). سنن أبي داود : كتاب الصلاة | باب : تفريع أبواب شهر رمضان | باب : في قيام شهر رمضان : 1371
قال ابن حجر العسقلاني:
"والأمر" (على ذلك) أي: على ترك الجماعة في التراويح، ولأحمد من رواية ابن أبي ذئب عن الزهري في هذا الحديث: "ولم يكن رسول الله(ص) جمع الناس على القيام".
Bayan Ibn Hajar Al-Askani ya tabbatar da Khalifa Umar ne ya kirkiro jam'in Tarawihi, sai kuma ya tabbatar da rashin ingancin Hadisin da ya nuna an yi jam'in Tarawihi a lokacin Annabi(saw); kuma Annabi(saw) ya yi marhabin da hakan:
وأما ما رواه ابن وهب عن أبي هريرة: " خرج رسول الله(ص) وإذا الناس في رمضان يصلون في ناحية المسجد فقال: ما هذا؟ فقيل: ناس يصلي بهم أبي بن كعب، فقال: أصابوا ونعم ما صنعوا ". ذكره ابن عبد البر، وفيه مسلم بن خالد وهو ضعيف، والمحفوظ أن عمر هو الذي جمع الناس على أبي بن كعب. (فتح الباري بشرح صحيح البخاري : 2009).
Babban malamin Ahlus-Sunnah الباجي (wanda ya yi Sharhin موطأ مالك) ya nakalto ابن حبيب ya na tabbatar ba'a yin Jam'in Tarawihi a lokacin Annabi(saw) da Khalifa Abubakar:
قال ابن حبيب رغب النبي(ص) في قيام رمضان من غير أن يأمر فيه بعزيمة فقام الناس وحدانا منهم في بيته ومنهم في المسجد فمات النبي(ص) وهم على ذلك وكان الناس على ذلك في خلافة أبي بكر وصدرا من خلافة عمر ثم رأى عمر أن يجمعهم فأمر أبيا وتميما الداري أن يصليا بهم... (المنتقى شرح موطأ مالك : الباجي : 300).
Malamin Ahlus-Sunnah أبو العلاء محمد عبد الرحمن ya tabbatar sai a lokacin Khalifancin Umar ne aka kirko jam'in Tarawihi:
قال أبو العلاء محمد عبد الرحمن: (والأمر على ذلك)أي على ترك الجماعة في التراويح وصدرا من خلافة عمر بن الخطاب، أي في أول خلافته وصدر الشيء ووجهه أوله، ثم جمع عمر(ر) الناس على قارئ واحد. (تحفة الأحوذي بشرح جامع الترمذي : 808).
Ibn Sa'd (Babban malamin Ahlus-sunnah), a littafin sa "Tabaqat" (j 3, s 281), ya na cewa:
"A shekara ta 14 bayan Hijira Umar ya kirkiri Jam'in Tarawihi":
وهو أول من سن قيام شهر رمضان وجمع الناس على ذلك وكتب به إلى البلدان وذلك في شهر رمضان سنة أربع عشرة وجعل للناس بالمدينة قارئين قارئا يصلي بالرجال وقارئا يصلي بالنساء...
Kenan sai da Annabi(saw) ya yi Shahada da shekara 4 sannan aka fara Jam'in Sallar Tarawihi a Masallatai? Kuma hakan ya tabbatar mana cewa lokacin khalifanci Abubukar ba'a yin sallar Tarawihi a jam'i.
Wannan ne ya sa Umar bai boye ba; ya kira Jam'in Tarawihi da bidi'ah; don ba'a yinsa a lokacin Annabi(saw) da Abubakar.
Al-Suyuti ya tabbatar Umar ne ya kirki jam'in tarawihi, a "Tarikh al-Khulafa", shafina 137. Hakama Al-Ayni, a Umdatul Qari (Sharh Sahihul Bukhari), j 6, s 125...:
ﺫﻛﺮ ﺍﻟﺴﻴﻮﻃﻲ ﻓﻲ ﻛﺘﺎﺑﻪ ﺗﺎﺭﻳﺦ ﺍﻟﺨﻠﻔﺎﺀ ﺃﻭﻟﻴﺎﺕ ﻋﻤﺮ ﻧﻘﻼ ﻋﻦ ﺍﻟﻌﺴﻜﺮﻱ ﻗﺎﻝ: ...ﻫﻮ ﺃﻭﻝ ﻣﻦ ﺳﻦ ﻗﻴﺎﻡ ﺷﻬﺮ ﺭﻣﻀﺎﻥ ﺑﺎﻟﺘﺮﺍﻭﻳﺢ ﻭﺃﻭﻝ ﻣﻦ ﺣﺮﻡ ﺍﻟﻤﺘﻌﺔ، ﻭﺃﻭﻝ ﻣﻦ ﺟﻤﻊ ﺍﻟﻨﺎﺱ ﻓﻲ ﺻﻼﺓ ﺍﻟﺠﻨﺎﺋﺰ ﻋﻠﻰ ﺃﺭﺑﻊ ﺗﻜﺒﻴﺮﺍﺕ...
Al-Askalani ya ce; Umar ya kira jam'in tarawihi da bidi'a; saboda Annabi(saw) bai sunnanta shi ba, hakama a lokacin Abubakar ba'a yin jam'in. Kuma bidi'ah ne yin jam'in sallar a farkon Dare, da kayyade adadinta (raka'a 11)...:
ﻗﺎﻝ ﺍﻟﻌﻼﻣﺔ ﺍﻟﻘﺴﻄﻼﻧﻲ ﻓﻲ ﺃﻭﻝ ﺍﻟﺼﻔﺤﺔ ﺍﻟﺮﺍﺑﻌﺔ ﻣﻦ جزﺀ ﺍﻟﺨﺎﻣﺲ ﻣﻦ ﺇﺭﺷﺎﺩ ﺍﻟﺴﺎﺭﻱ ﻓﻲ ﺷﺮﺡ ﺻﺤﻴﺢ ﺍﻟﺒﺨﺎﺭﻱ ﻋﻨﺪ ﺑﻠﻮﻏﻪ ﺇﻟﻰ ﻗﻮﻝ ﻋﻤﺮ ﻓﻲ ﻫﺬﺍ ﺍﻟﺤﺪﻳﺚ: ﻧﻌﻤﺖ ﺍﻟﺒﺪﻋﺔ ﻫﺬﻩ، ﻫﺬﺍ ﻟﻔﻈﻪ: ﺳﻤﺎﻫﺎ ﺑﺪﻋﺔ ﻷﻥ ﺭﺳﻮﻝ ﺍﻟﻠﻪ(ﺹ) ﻟﻢ ﻳﺴﻦ ﻟﻬﻢ ﺍﻻﺟﺘﻤﺎﻉ ﻟﻬﺎ، ﻭﻻ ﻛﺎﻧﺖ ﻓﻲ ﺯﻣﻦ ﺍﻟﺼﺪﻳﻖ. ﻭﻻ ﺃﻭﻝ ﺍﻟﻠﻴﻞ، ﻭﻻ ﻫﺬﺍ ﺍﻟﻌﺪﺩ ﺍﻟﺦ. ﻭﻓﻲ ﺗﺤﻔﺔ ﺍﻟﺒﺎﺭﻱ ﻭﻏﻴﺮﻩ ﻣﻦ ﺷﺮﻭﺡ ﺍﻟﺒﺨﺎﺭﻱ.
JAKANCI NE SALLAR TARAWIHI A JAM'I - INJI DAN KHALIFA UMAR IBN KHATTAB (ABDULLAHI IBN UMAR); KAMAR YANDA IBN ABI SHAIBA, AS-SAM'ANI... (MANYAN MALAMAN AHLUS-SUNNAH) SU KA RIWAITO.
Abdullah Ibn Umar ya tabbatar da jam'in Tarawihi bidi'ah ne, kuma ya yiwa babansa tawaye akan kirkirar bidi'ar jam'in Tarawihi.
Wata Rana wani mutum ya tambayi Abdullah Ibn Umar akan shin ya fi Lada ne in yi sallar Tarawihi a jam'i? Sai Ibn Umar ya ce; idan ka iya karatun Qur'ani ka yi sallar ka a gidanka ya fi Lada. Jakanci ne Sallar Tarawihi a Jam'i:
7742 - عبد الرزاق عن الثوري عن منصور عن مجاهد قال:جاء رجل الى ابن عمر؛ قال: أصلي خلف الامام في رمضان؟ قال: أتقرأ القرآن قال: نعم. قال: أفتنصت كأنك حمار. صلي في بيتك. - المصنف (للصنعاني) ج 4 / ص 264. المصنف (لابن ابي شيبة) ج 5 /ص232. ﺭﻭﺍﻩ ﺍﻟﻄﺤﺎﻭﻱ ﻓﻲ ﻣﻌﺎﻧﻲ ﺍﻵﺛﺎﺭ 1 / 351 ، ﻭﺍﻟﺼﻨﻌﺎﻧﻲ ﻓﻲ ﻣﺼﻨﻔﻪ ﺑﺮﻗﻢ 7742، 7797 ﻭﺳﻨﺪﻩ ﺻﺤﻴﺢ).
Abdullah Ibn Umar ba ya yin Sallar Tarawihi a jam'i:
ﻭﻓﻴﻪ ﻋﻦ ﻧﺎﻓﻊ ﻋﻦ ﺑﻦ ﻋﻤﺮ(ﺭ) ﺃﻧﻪ: ﻛﺎﻥ ﻻ ﻳﺼﻠﻰ ﺧﻠﻒ ﺍﻹﻣﺎﻡ ﻓﻲ ﺭﻣﻀﺎﻥ. - المصنف : عبد الرزاق الصنعاني، ج : ٤، ٢٨١. تاريخ الوفاة : ٢١١. تحقيق : تحقيق وتخريج وتعليق : حبيب الرحمن الأعظمي.
Karanta Sura daya ya fi lada akan bin jam'in Tarawihi:
ﻋﻦ ﺇﺑﺮﺍﻫﻴﻢ ﻗﺎﻝ: ﻟﻮ ﻟﻢ ﻳﻜﻦ ﻣﻌﻲ ﺍﻻ ﺳﻮﺭﺓ ﻭﺍﺣﺪﺓ ﻟﻜﻨﺖ ﺃﻥ ﺃﺭﺩﺩﻫﺎ ﺃﺣﺐ ﺍﻟﻰ ﻣﻦ ﺃﻥ ﺃﻗﻮﻡ ﺧﻠﻒ ﺍﻹﻣﺎﻡ ﻓﻲ ﺭﻣﻀﺎﻥ.
Imam ﺍﻟﻄﺤﺎﻭﻱ ya tabbtar da Tabi'ai da yawa ba sa bin jam'in Tarawihi:
ﻗﺎﻝ ﺍﻟﻄﺤﺎﻭﻱ ﺣﺪﺛﻨﺎ ﻳﻮﻧﺲ ﻗﺎﻝ ﺛﻨﺎ ﺃﻧﺲ ﻋﻦ ﻋﺒﻴﺪ ﺍﻟﻠﻪ ﺑﻦ ﻋﻤﺮ ﻗﺎﻝ: ﺭﺃﻳﺖ ﺍﻟﻘﺎﺳﻢ ﻭﺳﺎﻟﻤﺎ ﻭﻧﺎﻓﻌﺎ ﻳﻨﺼﺮﻓﻮﻥ ﻣﻦ ﺍﻟﻤﺴﺠﺪ ﻓﻲ ﺭﻣﻀﺎﻥ ﻭﻻ ﻳﻘﻮﻣﻮﻥ ﻣﻊ ﺍﻟﻨﺎﺱ...
Idan mun dauka hadisin riko da Sunnar khulafa'ur-Rashidin ya inganta, kuma khulafa'ur-Rashidin din su ne Abubakar, Umar, Usman da Imam Ali(as), to sunnar waye zamu yi riko da ita? Mai hana jam'in tarawihi ko mai cewa bidi'ah ne?
Shin Annabi(saw) ne ya bawa khalifa damar ya kirkiro Bidi'ah, kuma shi da kansa khalifan ya yi ikirarin bidi'a ce, sannan ayi riko da shi? Idan riko da sunnar khulafa'ur-Rashidin dole ne, kuma Imam Ali(as) ya na cikinsu, to me makomar wanda ya yi tawaye ga Imam Ali(as) har ya yake shi a Jamal, Siffin da Nahrawan?
Idan har Umar zai kirkiro Bidi'ah, kuma shi da kansa ya tabbatar da Bidi'ah ce, to menene hukunci koyi da shi akai; alhali Allah ya na cewa:
"Wadanda su ke sabawa (Annabi(saw) su yi saunar wata fitina ta same su, ko kuwa wata azaba mai radadi ta same su":
فَلْيَحْذَرِ الَّذِينَ يُخَالِفُونَ عَنْ أَمْرِهِ أَن تُصِيبَهُمْ فِتْنَةٌ أَوْ يُصِيبَهُمْ عَذَابٌ أَلِيمٌ (النور : 63).
"Kuma ba ya halatta ga Mumini ko Mumina, a lokacin da Allah da Annabi(saw) Ya hukunta wani umurni, wani zabi daga al'amarinsu ya kasance a gare su. Kuma wanda ya sabawa Allah da ManzonSa, to, ya bata, bata bayyananna":
وَمَا كَانَ لِمُؤْمِنٍ وَلَا مُؤْمِنَةٍ إِذَا قَضَى اللَّهُ وَرَسُولُهُ أَمْرًا أَن يَكُونَ لَهُمُ الْخِيَرَةُ مِنْ أَمْرِهِمْ ۗ وَمَن يَعْصِ اللَّهَ وَرَسُولَهُ فَقَدْ ضَلَّ ضَلَالًا مُّبِينًا (الاحزاب : 36).
Idan kun ce akwai hadisan da su ke alamta Annabi(saw) ya yi jam'in Sallar nafila a dararen Ramadan, mu kaddara sun inganta, wacce ya yi; tarawihi ko tahajjud?
Me sa ya daina daga baya?
Idan kun ce saboda tsoron kar a farlanta; kenan sai Annabi(saw) ya yi wani abu sannan Allah zai san ko ya kamata ya wajabta shi ko a'a?
Kenan Annabi(saw) ya na yin abubuwa akan sun ransa ba tare da umarnin Allah(swt) ba?
Idan duk abinda Annabi(saw) ya yi umarni ne daga Allah(swt); kenan Allah(swt) ne ya yi masa umarnin ya yi jam'in?
To me ya sa zai dena kuma ya kafa hujja da cewa ya na jin tsoron kada a wajabta?
Allah(swt) ne ya ke wajebta abinda ya ke so ko Annabi(saw) ne ya ke bawa Allah(swt) umarnin abinda zai wajabta?
Ya zamu yi da inganttun hadisai masu yawan gaske da suke kwadaitarwa da yin sallar nafila a gida a madadin Masallatai?
Ko a hadisan an nuna banda a Ramadan?
Kenan ba wata hujja da ta ke alamta a wajen Ramadan ake nufi? Sai dai in tawili za'a yi?
Sahabi Zaid Ibn Sabit ya riwaito Annabi(saw) ya na cewa; yin Sallar Nafila a gida (ba tare da yin jam'i ba) ta fi lada akan yinta a Masallaci:
1044 حَدَّثَنَا أَحْمَدُ بْنُ صَالِحٍ، حَدَّثَنَا عَبْدُ اللَّهِ بْنُ وَهْبٍ، أَخْبَرَنِي سُلَيْمَانُ بْنُ بِلَالٍ، عَنْ إِبْرَاهِيمَ بْنِ أَبِي النَّضْرِ، عَنْ أَبِيهِ، عَنْ بُسْرِ بْنِ سَعِيدٍ، عَنْ زَيْدِ بْنِ ثَابِتٍ، أَنَّ رَسُولَ اللَّهِ(ص)َ قَالَ: "صَلَاةُ الْمَرْءِ فِي بَيْتِهِ أَفْضَلُ مِنْ صَلَاتِهِ فِي مَسْجِدِي هَذَا، إِلَّا الْمَكْتُوبَةَ". - صحيح البخاري ( 731, 6113, 7290 ). - صحيح مسلم ( 781 )
- سنن أبي داود : كتاب الصلاة | تفريع أبواب الركوع والسجود | باب : صلاة الرجل التطوع في بيته ( 1447 ). - سنن الترمذي ( 450 )
- سنن النسائي ( 1599 ). - موطأ مالك ( 344 ). - سنن الدارمي ( 1406 ). - مسند أحمد ( 21582, 21603, 21624, 21632 ).
A wata ruwaya, Zaid Ibn Sabit ya riwaito Annabi(saw) ya na cewa;
"Ku rika yin sallar (Nafila) a gidajenku, sallar mutum a gidansa tafi (lada akan sallarsa a Masallaci) sai dai in sallar farilla ce":
عن ﺯﻳﺪ ﺑﻦ ﺛﺎﺑﺖ ﺃﻥ ﺍﻟﻨﺒﻲ(ص) ﻗﺎﻝ ﻓﻲﻗﻴﺎﻡ ﺭﻣﻀﺎﻥ: ﺃﻳﻬﺎ ﺍﻟﻨﺎﺱ، ﺻﻠﻮﺍ ﻓﻲ ﺑﻴﻮﺗﻜﻢ؛ ﻓﺈﻥ ﺃﻓﻀﻞ ﺻﻼﺓ ﺍﻟﻤﺮﺀ ﻓﻲ ﺑﻴﺘﻪ ﺇﻻ ﺍﻟﻤﻜﺘﻮﺑﺔ.
- ﻣﺘﻔﻖ ﻋﻠﻴﻪ (ﺡ 447 ). ﺍﻟﻠـﺆﻟـﺆ ﻭﺍﻟﻤﺮﺟﺎﻥ ﻓﻴﻤﺎ ﺍﺗﻔﻖ ﻋﻠﻴﻪ ﺍﻟﺸﻴﺨﺎﻥ ( 1/166 /167–ﺡ 447 ) . ﺇﺳﻨﺎﺩﻩ ﺻـﺤﻴـﺢ ، ﺃﺧﺮﺟﻪ ﺃﺑﻮ ﺩﺍﻭﺩ( 1044 ) ﺑـﻠـﻔﻆ: ﺻﻼﺓ ﺍﻟﻤﺮﺀ ﻓﻲ ﺑﻴﺘﻪ... ﻭﺍﻟﺒﻐﻮﻱ ﻓﻲ ﺷﺮﺡ ﺍﻟﺴﻨﺔ: 4/130 131- /ﺡ 995 ،996.
ﺍﻟﻨﺴﺎﺋﻲ - ﺍﻟﺴﻨﻦ ﺍﻟﻜﺒﺮﻯ - ﺍﻟﺠﺰﺀ : ( 1 ) - ﺭﻗﻢ ﺍﻟﺼﻔﺤﺔ : ( 159 )
ﺳﻨﻦ ﺍﻟﺘﺮﻣﺬﻱ - ﺍﻟﺼﻼﺓ - ﻣﺎ ﺟﺎﺀ ﻓﻲ ﻭﺻﻒ .. - ﺭﻗﻢ ﺍﻟﺤﺪﻳﺚ ( 403 ).
Al-Nasa'i, a Sunan, j 3, s 161 - 198, ya riwaito Annabi(saw) ya na cewa:
صلاة ﺍﻟﻤﺮﺀ ﻓﻲ ﺑﻴﺘﻪ ﺃﻓﻀﻞ ﻣﻦ ﺻﻼﺗﻪ ﻓﻲ ﻣﺴﺠﺪﻱ ﻫﺬﺍ ﺇﻻ ﺍﻟﻤﻜﺘﻮﺑﺔ
"Sallar mutum (ta Nafila) a gidansa tafi (lada) akan sallar Nafila a Masallacin Annabi(saw)".
- ﺇﺳﻨﺎﺩﻩ ﺻﺤﻴﺢ، ﺃﺧﺮﺟﻪ ﺃﺑﻮ ﺩﺍﻭﺩ ( 1044) ﻭﺍﻟﺒﻐﻮﻱ ﻓﻲ ﺷﺮﺡ ﺍﻟﺴﻨﺔ( ﺡ 966-965 ).
ﺳﻨﻦ ﺃﺑﻲ ﺩﺍﻭﺩ - ﺍﻟﺼﻼﺓ - ﺻﻼﺓ ﺍﻟﻠﻴﻞ - ﺭﻗﻢ ﺍﻟﺤﺪﻳﺚ : ( 1143 ). ﺍﻹﻣﺎﻡ ﻣﺎﻟﻚ - ﻛﺘﺎﺏ ﺍﻟﻤﻮﻃﺄ - ﻧﺪﺍﺀ ﺍﻟﺼﻼﺓ - ﺻﻼﺓ ﺍﻟﻨﺒﻲ ( ﺹ ) - ﺭﻗﻢ ﺍﻟﺤﺪﻳﺚ : ( 243 ).
Masallacin Annabi(saw) da ya ke na 2 a daraja a dukkan Masallatan Duniya, amma Annabi(saw) ya ce; sallar Nafila a gida tafi sallah a cikinsa lada.
Al-Nawawi, a sharhin Sahih Muslim, ya kawo ra'yoyin malaman Ahlus-Sunnah akan jam'in Sallar tarawihi, har zuwa inda ya ke cewa;
"Imam Malik, Abu Yusuf, wasu malaman Shafi'iyya sun ce; ya fi lada mutum ya yi sallar Tarawihi (a gida) shi kadai, sun tabbatar yin Sallar Tarawihi ba'a Jam'i ba ya fi lada; saboda an riwaito Annabi(saw) ya na cewa: "Sallar Nafila a gida (ba tare da yin jam'i ba) ta fi lada akan yinta a Masallaci":
قال النووي: ...وقال مالك وأبو يوسف وبعض الشافعية وغيرهم: الأفضل فرادى في البيت؛ لقوله(ص): "أفضل الصلاة صلاة المرء في بيته إلا المكتوبة". (المنهاج شرح صحيح مسلم بن الحجاج : 759، 174).
An-Nawawi ya kara da cewa; an fi son mutum ya yi sallar Nafila a gida saboda hakan ya fi nuna mutum don Allah ya yi, hakan ya na sa gida ya yi albarka, rahma ta sauka, a kori Shaidan daga gidan...:
قال النووي: "إنما حث على النافلة في البيت لكونه أخفى وأبعد من الرياء وأصون من محبطات الأعمال وليتبرك البيت بذلك وتنزل فيه الرحمة والملائكة وينفر منه الشيطان...". (عون المعبود شرح سنن أبي داود : 1044).
Kenan Jam'in sallar tarawihi a Masallatai ya sabawa Sunnah da umarnin Annabi(saw); saboda Annabi(saw) ya yi umarni da mu rika yin sallar Nafila a gidajenmu a madadin muje masallaci, hakan shi zai sa karin albarka a gidajenmu?
Imam Baqir(as) da Imam Sadiq(as) sun tabbatar da cewa; jam'in sallar tarawihi bidi'a ne:
(Al-Hurr al-Amili, Wasa’il, j 8, s 45).
ﺭﻭﻯ ﺍﻟﺸﻴﺦ ﺍﻟﻄﻮﺳﻲ ﻓﻲ ﺍﻟﺘﻬﺬﻳﺐ ﺑﺴﻨﺪ ﻣﻌﺘﺒﺮ ﻋﻦ ﻋﻤّﺎﺭ، ﻋﻦ ﺃﺑﻲ ﻋﺒﺪ ﺍﻟﻠّﻪ(ع)، ﻗﺎﻝ: ﺳﺄﻟﺘﻪ ﻋﻦ ﺍﻟﺼﻼﺓ ﻓﻲ ﺭﻣﻀﺎﻥ ﻓﻲ ﺍﻟﻤﺴﺎﺟﺪ؟ ﻗﺎﻝ: ﻟﻤّﺎ ﻗﺪﻡ ﺃﻣﻴﺮ ﺍﻟﻤﺆﻣﻨﻴﻦ(ع) ﺍﻟﻜﻮﻓﺔ ﺃﻣﺮ ﺍﻟﺤﺴﻦ ﺑﻦ ﻋﻠﻲ(ع) ﺃﻥ ﻳﻨﺎﺩﻱ ﻓﻲ ﺍﻟﻨﺎﺱ: ﻻ ﺻﻼﺓ ﻓﻲ ﺷﻬﺮ ﺭﻣﻀﺎﻥ ﻓﻲ ﺍﻟﻤﺴﺎﺟﺪ ﺟﻤﺎﻋﺔ.
Shaikh At-Tusi ya ruwaito a Tahzib... Daga Abu Abdullah(as), an tambayi shi hukunci sallar Tarawihi (a jam'i), sai ya ce; lokacin da Imam Ali(as) ya zo Kufa (Iraq) ya umurci Imam Hasan(as) da ya yi shelar cewa; (babu lada) a yin jam'in sallar (Tarawihi) a Masallatai, (sai dai in sallar farilla ce).
Al-Shawkani, Nayl al-Autar, j 3, s 50, ya tabbatar da bidi'a ne jam'in sallar tarawihi:
ﺍﻟﺸﻮﻛﺎﻧﻲ: ﻗﺎﻝ ﻣﺎﻟﻚ ﻭﺍﺑﻮ ﻳﻮﺳﻒ ﻭﺑﻌﺾ ﺍﻟﺸﺎﻓﻌﻴﺔ ﻭﻏﻴﺮﻫﻢ، ﺍﻷﻓﻀﻞ ﻓﺮﺍﺩﻯ ﻓﻲ ﺍﻟﺒﻴﺖ ﻟﻘﻮﻟﻪ(ﺹ): ﺍﻓﻀﻞ ﺍﻟﺼﻼﺓ ﺻﻼﺓ ﺍﻟﻤﺮﺀ ﻓﻲ ﺑﻴﺘﻪ ﺇﻻ ﺍﻟﻤﻜﺘﻮﺑﺔ، ﻣﺘﻔﻖ ﻋﻠﻴﻪ. ﻭﻗﺎﻟﺖ ﺍﻟﻌﺘﺮﺓ: ﺇﻥ ﺍﻟﺘﺠﻤﻊ ﻓﻴﻬﺎ ﺑﺪﻋﺔ...
Shin hadisan da su ke alamta abar mata da yara su ke zuwa Masallatai; su na nufin don yin jam'in sallar farilla ne ko nafila?
Shin a hadisan an ambaci jam'in sallar tarawihi?
Kasantuwar zuwa Tarawihi da tahajjud ya ya na bawa wasu samari da 'yan mata damar aikata Al-fasha, kuma jam'in bidi'a ne, hakan bai isa dalilin da zai sa jam'in sallar tarawihi da tahajjud ya zama kofar fasadi ba? Doriya akan shiga hakkin makota da suke kusa da Masallatan da ake hanasu barci da dare?
Barema a wasu Ingantattun hadisai Annabi(saw) ya tabbatar da Sallar mace a dakin mijin ta ya fi lada fiye da Sallah tare da Annabi(saw) a Masallaci:
Idan Sallar mace a dakin mijin ta ya fi lada fiye da Sallah tare da Annabi(saw) a Masallaci; to ina ta kuma a bayan wani gardi (kato)?
27090 حَدَّثَنَا هَارُونُ، حَدَّثَنَا عَبْدُ اللَّهِ بْنُ وَهْبٍ، قَالَ: حَدَّثَنِي دَاوُدُ بْنُ قَيْسٍ، عَنْ عَبْدِ اللَّهِ بْنِ سُوَيْدٍ الْأَنْصَارِيِّ، عَنْ عَمَّتِهِ أُمِّ حُمَيْدٍ - امْرَأَةِ أَبِي حُمَيْدٍ السَّاعِدِيِّ - أَنَّهَا جَاءَتِ النَّبِيَّ(ص)َ، فَقَالَتْ: يَا رَسُولَ اللَّهِ، إِنِّي أُحِبُّ الصَّلَاةَ مَعَكَ. قَالَ: "قَدْ عَلِمْتُ أَنَّكِ تُحِبِّينَ الصَّلَاةَ مَعِي، وَصَلَاتُكِ فِي بَيْتِكِ خَيْرٌ لَكِ مِنْ صَلَاتِكِ فِي حُجْرَتِكِ، وَصَلَاتُكِ فِي حُجْرَتِكِ خَيْرٌ مِنْ صَلَاتِكِ فِي دَارِكِ، وَصَلَاتُكِ فِي دَارِكِ خَيْرٌ لَكِ مِنْ صَلَاتِكِ فِي مَسْجِدِ قَوْمِكِ، وَصَلَاتُكِ فِي مَسْجِدِ قَوْمِكِ خَيْرٌ لَكِ مِنْ صَلَاتِكِ فِي مَسْجِدِي". قَالَ: فَأَمَرَتْ، فَبُنِيَ لَهَا مَسْجِدٌ فِي أَقْصَى شَيْءٍ مِنْ بَيْتِهَا وَأَظْلَمِهِ، فَكَانَتْ تُصَلِّي فِيهِ، حَتَّى لَقِيَتِ اللَّهَ عَزَّ وَجَلَّ.
حكم الحديث: حديث حسن، صحيح.
- مسند أحمد : مسند النساء | حديث أم حميد : 27090.
- سنن أبي داود : كتاب الصلاة | باب : التشديد في ذلك : 570.
Comments
Post a Comment